Sudan na cikin kasashen Larabawa na Afirka kuma ta kasance karkashin mulkin mallaka na Birtaniya zuwa shekarar 1956.
Kasar ta yi fama da rikice-rikice gami da yake-yake har ta dare gida biyu a shekara ta 2011 bayan yakin basasa na tsawon lokaci tsakanin yankin arewaci da kudanci, inda aka samu sabuwar kasar Sudan ta Kudu wadda ta balle daga Sudan.