Sabuwar shugaban gwamnatin Jamus za ta fara ziyarar kasashen Turai. | Labarai | DW | 23.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabuwar shugaban gwamnatin Jamus za ta fara ziyarar kasashen Turai.

Sabuwar shugaban gwamnatin tarayyar Jamus, Angela Merkel, za ta fara ziyarar manyan biranen kasashen Turai a yau, kwana daya bayan an rantsad da ita a sabuwar mukaminta. Rahotanni dai sun nuna cewa, a yau laraba, za ta fara kai ziyara ne a biranen Paris da Brussels, inda za ta gana da shugabannin kasashen Faransa da na Belgium. Sa’annan a gobe ne kuma za ta kai ziyara a birnin London don yin shawarwari da mahukuntan Birtaniya. Muhimman batutuwan da ke kan ajandar tattaunawar da za ta yi sun hada ne da batun kasafin kudin kungiyar Tarayyar Turan nan da har ila yau ake ta korafi a kansa.

Tuni dai shugaba Chirac na Faransa, ya kyautata zaton cewa, Angela Merkel, za ta ci gaba da inganta hulda tsakanin Faransa da Jamus, duk da alamun da ta nuna na cewa, za ta fi mai da hankali ne wajen kyautata dangantaka da Amirka.

A jiya ne dai aka rantsad da sabuwar shugaban gwamnatin, wadda kuma ita ce mace ta farko da ta taba rike wannan mukamin a tarihin Jamus. Za ta jagoranci gwamnatin hadin gwiwa ne tsakanin jam’iyyarta ta CDU da jam’iyyar Social Democrats, wadda ta ja ragamar mulki kafin zaben da aka yi a cikin watan Satumba.