Sabon fata kan batun nukiliyar Iran | Labarai | DW | 10.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon fata kan batun nukiliyar Iran

Sakataren harkokin kasashen ketare na Amirka John Kerry ya ce sun samu ci gaba mai ma'ana a tattaunawar da suke tsakaninsu da Iran kan batun makamashin nukiliyarta.

Kerry ya bayyana hakan ne ga manema labarai inda ya ce sun warware muhimman batutuwa da dama da a baya suka nemi su kawo tarnaki a game da batun cimma matsaya. Dama dai tuni shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana cewa ya yi amanna za a kai ga cimma matsaya a tattaunawar da suke yi da Iran din kan batun nukiliyar. Kasashen Amirka da Rasha da China da Birtaniya da Faransa da kuma Jamus dai sun kara wa'adin tataunawar ta su da Iran zuwa ranar Litinin din mako mai zuwa bisa fatan cewa za su warware dukkan batutuwan da ke neman kawo musu cikas a tattaunawar da suka dade suna fatan cimma dai-daito a tsakaninsu a kanta. Tuni dai kungiyar EU ta bayyana kara wa'adin takunkumin da ta dagewa Iran din na wani lokaci a baya, zuwa ranar Litinin 13 ga wannan wata na Yuli da muke ciki domin ba da damar samun nasara a tattaunawar.