Merkel ta yaba da bunkasar tattalin Jamus | Labarai | DW | 30.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Merkel ta yaba da bunkasar tattalin Jamus

Matsayin tattalin arzikin Jamus da sabunta makamashi na daga cikin manyan batutuwan da shugabar gwamnatin ta gabatar a gaban majalisar dokoki ta Bundestag.

A jawabinta na farko a majalisar tarayya ta Bundestag, bayan darewarta karagar mulki a karo na uku, shugabar gwamnati Angela Merkel ta yi tsokaci kan batutuwa masu muhimmanci na cikin gida da kuma tattalin arziki. Ta yi bayani dangane da bunkasar tattalin arzikin Jamus daga matsin tattali da duniya ta tsinci kanta a ciki, a matsayin kasar na wadda ta fi kowacce karfin tattali a nahiyar Turai. Merkel ta yaba wa raguwar yawan marasa aikin yi, da kaddamar da mafi kankancin albashi da ake shirin yi a nan tarayyar Jamus. Kazalika shugabar gwamnatin ta Jamus ta sake jaddada bukatar hadin kai tsakanin kasashen Turai domin a tafi tare a tsira tare.

A cewarta wannan hadin kan ne ya kawo zaman lafiya da walwala da martaba 'yanci.

Mekel haila yau ta yi Allah wadan Amurka da Britaniya dangane da zargin da ake musu na leken asiri, sai dai 'yan adawa sun ce hakan bai isa.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Umaru Aliyu