1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar dokokin Jamus ta yi muhawara kan batancin da aka yi wa annabi Muhammadu, tsira da maincin Allah su tabbata a gare shi.

February 10, 2006

A yau ne majalisar dokkoin Jamus, wato Bundestag, ta yi muhawara kan batun nan da ya janyo bacin ran musulmi a duniya naki daya, wato na buga zanen siffanta annabi Muhammadu, salal lahu alaihi wassalam, da wasu hotunan zanen da aka buga a jaridun kasashen yamma.

https://p.dw.com/p/Bu1n
Zauren taron majalisar dokoki ta Bundestag
Zauren taron majalisar dokoki ta BundestagHoto: AP

Wakilan duk jam’iyyun na Bundestag sun nuna rashin amincewarsu da tashe-tashen hankullan da suka wakana a wasu kasashe, a zanga-zangar da musulmi suka yi a duniya baki daya, don nuna bacin ransu da zanen hotunan nan da ke nuna wulakanci ga addininsu.

Jam’iyyar adawa ta Greens ce ta bukaci a yi wannan muhawarar. Da yake gabatad da jawabinsa, shugaban reshen jam’iyyar a Majalisar, Fritz Kuhn, ya ce babu shakka, wajibi ne jama’a su yi zanga-zanga don nuna bacin ransu, kuma hakkinsu ne. Amma, tashe-tashen hankulla da suka biyo bayan zanga-zangar a wasu wurare , ba abin da ya dace ba ne. Kamar dai yadda ya bayyanar:-

„Wanda ya yunkuri nuna wulakanci ga annabi Muhammadu, ta hanyar zane, inda ya kwatanta shi da dan ta’adda, to fa ya san yana nuna wulakanci ne ga dimbin yawan musulmi, har da ma na nan Turai, wadanda ba sa tashe-tashen hankulla, suke kuma nisantad da kansu daga duk ire-iren ayyukan ta da zaune tsaye. Sabili da haka ne nake ganin wannan zanen tamkar nunin wariya.“

Amma kuma, shugaban na reshen jam’iyyar Greens a majalisar ya nanata cewa:-

„Babu shakka, `yancin fadar albarkacin baki, wato wani abu ne da muke daukarsa da muhimmanci. To hauhawar tsamarin da ake samu, na neman wani mizanin cim ma daidaito, ita ce babbar matsalar wannan muhawarar. Wajibi ne mutane su yi zanga-zangar nuna adawarsu ga wannan wautar, da aka yi a kasar Denmark. Amma bai kamata wasu hukumomin kasashe dai-dai, `yan kama karya, maras bin tafarkin dimukradiyya su yi amfani da wannan damar wajen angaza jama’a yin tarzoma ba.“

Duk jam’iyyun dai sun yarje kan cewar, `yancin maneman labarai da fadar albarkacin baki, zaunannun ka’idoji ne da ba za a kau da su ba. Wasu `yan majalisar dai, sun ce ba su ga dalilin da ya sa ba za a iya buga labaran da ba su da dadin ji ba. A ganin Nils Annen, dan jam’iyyar SPD ma, wato kaskantad da kai ne, neman gafarar da wani zababben shugaban gwamnati ya yi, saboda abin da wata jaridar kasarsa ta buga:-

„A ganina dai, bai dace ba ko kadan, a ce wani shugaban gwamnatin da aka zaba ta hanyar dimukradiyya, ya fito fili ya nemi gafara game da abin da wata jairdar kasarsa ta buga. Wannan nuna wulakanci ne da kaskantad da kai.“

A nan dai, dan majalisar na matashiya ne da bayanan da Firamiyan kasar Denmark ya yi wa maneman labarai na nuna nadamarsa ga rikicin da buga zanen da jaridar kasarsa ta yi, ya janyo. Wasu `yan majalisar ma sun bukaci Jamus ne ta nuna zumunci ga Denmark din ta karfafa mata gwiwa wajen daddage wa angaza mata da wasu kasashe ke son yi. Karl-Theodor von Guttenberg, dan jam’iyyar CDU, cewa ya yi a cikin jawabinsa:-

„Bai kamata mu kyale Denmark kadai, ta huskanci bukatun da wasu kasashe ke yi mata, ko kuma barazanar katse duk wasu huldodin kasuwancin da Iran ke yi mata ba. A nan dai wajibi ne Denmark ta sami tabbacin cewa, muna nuna mata zumunci dari bisa dari.“

An dai kuma sami wadanda suka yi kira ga taka tsantsan, wajen daukan matsayi a kann wannan batun. Tsohon shugaban majalisar, kuma mataimakin shugaban na yanzu, Wolfgang Thierse na jam’iyar SPD, ya gargadi takwarorinsa `yan majalisa ne da su guji yin amfani da wannan rikicin wajen neman wata fa’ida ga jam’iyyunsu. Yin hakan ba zai janyo halin zaman lafiya tsakanin addinai a nan Jamus, da Turai da ma duniya baki daya ba, inji shi. Shi dai Thierse, a fakaice, yana matshiya ne da wani yunkurin da jam’iyyun `yan mazan jiya na CDU da CSU ke yi, na jibinta tashe-tashen hankullan da aka yi a kasashen musulmi a kan wannan batun, da neman da kasar Turkiyya ke yi na shiga cikin kungiyar Hadin Kan Turai.