Jamus tace kada Amurka ta kawo farraka tsakanin kasashen turai | Labarai | DW | 18.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus tace kada Amurka ta kawo farraka tsakanin kasashen turai

Manistan harkokin wajen Jamua Frank Walter Steinmeier ya gargadi kasar Amurka da kada ta kawo farraka tsakanin kasashen turai sakamakon shirinta na girke tashar kare makamai masu linzami a kasashen Poland da Czech.

Steinmeier ya fadawa wata jaridar lahadi lahadi ta nan Jamus cewa,akwai bukatar kasashen turai kada su bari wannan shiri na Bush ya janyo gaba tsakaninsu.

Kasar rasha dai tayi suka da kakkausar murya wannan shiri na gwamnatin Amurka,tana mai fadin cewa barazana ce ga tsaronta.

Nan gaba a yau Steinmeir zai kama hanyarsa ta zuwa birnin washington inda zai gana da takwararsa Condoleeza Rice.