Jamus ta yi gargadin yiwuwar yaki tsakanin NATO da Rasha
October 13, 2025
A lokacin da yake wannan gargadi a gaban majalisar dokoki ta Bundestag a Litinin din nan, shugaban hukumar leken asirin Jamus Martin Jäger ya ce Rasha ta yi imanin cewa za ta iya fadada tasirinta zuwa yammacin Turai domin ya koma yin dogaro da ita, kuma domin cimma wannan buri Moscow ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen shiga rikicin soji kai tsaye da NATO.
Mista Jäger ya kara da cewa bai kamata kasashen Turai su kwanta barci ba, domin da kowane lokaci Rasha na iya kaddamar musu duba da babin makura da aka shiga a halin yanzu.
Karin bayani: Berlin na zargin Moscow da yi wa nahiyar Turai barazana
Wannan gargadi na zuwa ne a daidai lokacin da take-taken Rasha ke kara fitowa fili, musamman kutse da ta yi wa sararin samaniyar wasu kasashen Turai da jirage maras matuka ciki har da Poland da Jamus, lamarin da ya kai kungiyar NATO ga yi mata kakkwaran kashedi amma kuma ta yi kunnen kashi.
Karin bayani: NATO ta gargadi Rasha kan keta sararin samaniyar mambobinta