1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Berlin na ci gaba da nuna wa Moscow 'yar yatsa

Abdoulaye Mamane Amadou
September 25, 2025

Gwamnatin Jamus ta bayyana yawaitar shawagin jiragen saman Rasha marasa matuka a matsayin babbar barazana ga nahiyar Turai

https://p.dw.com/p/514MI
Ministan cikin gidan Jamus Alexander Dobrindt
Ministan cikin gidan Jamus Alexander DobrindtHoto: dts-Agentur/picture alliance

Ministan cikin gidan Jamus, Alexander Dobrindt, ya bayyana cewa Jamus da sauran kasashen nahiyar Turai na cikin wani yanayi na kwambalar jirage maras matuka, tare da gargadin kasashen nahiyar game da karuwar barazanar Rasha.

Jamus ta yi allawadai da harin Rasha kan Poland

Tamkar wasu sauran kasashen Turai, Jamus ta sha fama da kutsen jirage maras matuka, da ke shafe tsawon lokaci suna shawagi a sararin samaniya da wasu muhimman gine-gine da cibiyoyinta, amma kuma ba tare da an san daga ina suke fitowa ba, sai dai kuma ministan na Jamus, ya nuna 'yar yatsa kan Moscow, wanda ya ce ita ce uwa da makarbiya.

Kokarin Turai na kawo karshen yakin Ukraine

Berlin na zargin Moscow da kara azama ne wajen ayyukan zagon kasa da leken asiri a kasashen da ba ta dasawa da su na nahiyar Turai, kamkar yadda hakan ya auku a kasar Denmark. A lokacin da yake jawabinsa a gaban majalisar dokoki ta Bunsdestag, Minista Dobrindt, ya ce kasar na kara karfafa matakan kare kanta daga ire-iren wannan barazana.