NATO kungiya ce ta tsaro da ta hada kan kasashen yammacin Turai da Amirka da Turkiyya da kuma Kanada.
Kungiyar NATO wato Kungiyar tsaron arewacin tekun Atlantika, tana aiki ne wajen kare kasashen da ke zaman mambobi a cikinta. An dai kafa ta ne shekaru hudu bayan da aka kammala yakin duniya na biyu. Yanzu haka kungiyar ta NATO na da mambobi 28.