Birtaniya ta ce za ta bukaci bayanai daga Amirka kan zargin da ake yi mata na kafa sansanonin kungiyar leken asirinta a Turai. | Labarai | DW | 23.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Birtaniya ta ce za ta bukaci bayanai daga Amirka kan zargin da ake yi mata na kafa sansanonin kungiyar leken asirinta a Turai.

Birtaniya ta ce tana shirin mika wa Amirka wata takarda bisa manufa, a madadin kungiyar Hadin Kan Turai, don neman bayanai game da wanzuwar wasu gidajen yari na sirri a nahiyar Turai, inda kungiyar leken asirin Amirkan, wato CIA ke azabtad da fursunoni. Ma’aikatar harkokin wajen Birtaniyan da ke birnin London, ta ce ta yanke shawarar yin hakan ne bayan wani taron da ministocin harkokin wajen kasashen EUn suka yi a birnin Brussels. kasashe da dama na kungiyar dai sun nuna damuwarsu ne game da gallaza wa fusunoni masu tsatsaurar ra’ayin islama da ke jami’an CIA din ke ta yi.

Kawo yanzu dai, mahukuntan birnin Washington, sun ki tabbta ko kuma karyata zargin da ake yi wa kungiyar leken asirin kasar, na kafa wasu sansanonin sirri a Turai, da Afghanistan, da Thailand da wasu wurare, inda take tsare da dubannin fursunoni, take ta kuma nuna musu azaba.