Taba Ka Lashe(19.04.2017)
April 20, 2017Talla
A shekarun baya malam Alhousseini Anivolla wanda makadin guitar kana mawaki ya kasance a cikin Kungiyar Etran Finatawa shahararriyar kungiyar gambizar makadan Abzinawa da filani ta kasar Nijar, kafin daga bisani ya koma yin aiki shi kadai. Kuma wannan sabon kundin waka mai suna OSAS shi ne kundin waka na biyu da ya buga shi kadai. To sai dai kuma wannan shi ne karo na farko da ya kaddamar da albun din wakokinsa a kasar Jamus.