Sudan ta karyata cewa ta hana jakadan Majalaisar dinkin duniya shiga Darfur | Labarai | DW | 04.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sudan ta karyata cewa ta hana jakadan Majalaisar dinkin duniya shiga Darfur

Gwamnatin kasar Sudan ta karyata cewa,ta haramtawa jakadan Majalisar Dinkin Duniya Jam Egeland zuwa yankin Darfur da yaki yayi kaca kaca da shi,amma tace,ta nemi a jinkirta ziyarar tasa ce saboda wasu matsaloli.

Wakilin maaikatar yada labarai ta Sudan Bekri Mula ya fadawa kanfanin dillancin labarai na AFP cewa,Sudan bata hama Egelanda zuwa Darfur ba,abinda tayyi shine jinkirta zuwan nasa saboda batun shirin aikawa da dakarun MDD zuwa darfur ne.

Tunda farko da can,Egeland zai fara ziyarar ce a jiya litinin domin ganewa idanuwansa yadda abubuwa suka tabarbare a yankin na Darfur,bayan shekaru 3 na yaki,kafin ya wuce zuwa birnin Khartoum,amma kuma MDD tace gwamnatin Sudan din tace bata maraba da shi.