Rashin tsaro da bazuwar makamai a yammacin Afirka
January 25, 2018Talla
Kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru har ma da Mali na fuskantar kalubale na rashin tsaro na hare-hare na 'yan ta'adda, sannan ga karuwar masu garkuwa da mutane don neman kudaden fansa, da kuma tashin hankali tsakanin manoma da makiyaya. Bazuwar makamai da ke yawo a yankin yammacin Afirka duk da irin matakan da ake dauka ya kara tinzura lamarin.