Ana cigaba da neman turawa da aka sace a Kaduna | Labarai | DW | 18.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana cigaba da neman turawa da aka sace a Kaduna

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da labarin sace wasu turawa biyu tare da halaka ‘yan sandan da ke yi musu rakiya a hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Turawan biyu 'yan kasashen Amirka da Kanada ne kamar yadda binciken da aka gudanar ya nunar. Rundunar ‘yan sandar jahar Kaduna ta watsa jami’an tsaro a daukacin yankin domin farautar wadanda suka sace wadannan turawan.

Sanarwa daga mahukuntan kasar Kanada da Amirka ta tabbatar da cewa an yi garkuwa da 'yan kasashen na su tare da cewa ana ci gaba da tattaunawa da gwamnatin Najeriya don ganin an yanto turawan da ransu.