Buhari bai ji dadin kashe-kashen Benue ba | Labarai | DW | 04.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Buhari bai ji dadin kashe-kashen Benue ba

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bayyana bacin rai kan rikice-rikice masu muni da ke aukuwa tsakanin makiyaya da kuma manoma a wasu sassan kasar, rigingimun da ke haddasa asarar rayukan 'yan kasar da dama.

Shugaba Buhari na magana ne bayan aukuwar wata rigima tsakanin manoma a Benue da ke tsakiyar kasar da kuma fulani makiyaya, inda aka yi zargin fulanin da kashe manoma akalla 20 a yankin karamar hukumar Guma. Daruruwan mutane ne dai suka yi ta zanga-zanga a Makurdi babban jihar ta Benue suna mai nuna fushi da wuce iyakar da makiyayan ke yi.

Sai dai a nasu bangaren makiyayan da ake zargi a Najeriya, na cewa ne kashe-kashen da barnar dukiyar da ake masu cikin dazukan kasar, na wucewa ne ba tare da ana sani ko kuma daukar mataki na doka ba.

Wasu rahotannin daga arewa maso gabashin Najeriyar, sun ce mayakan Boko Haram sun yi garkuwa da wasu matasa su 31 a yankin Gamborun jihar Borno. Majiyoyin tsaron kado-da-gora da yankin ne suka tabbatar da faruwar lamarin, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya ruwaito. Matasan da aka ce sun shiga dazukan Gamborun ne don neman itace sun shiga hannun mayakan  na Boko Haram ne, kwanaki kalilan da bacewar wasu sojoji 30, bayan wani farmaki da aka kai kan wani sansani na soji da ke yankin.