Najeriya: Kungiyar Miyetti Allah ta nuna damuwa
January 14, 2018Talla
Kungiyar Miyetti Allah ta Fulani Makiya a Najeriya, ta bukaci a hukunta duk wani wanda aka samu da hannu a kashe-kashen da suke faruwa da ake dangata 'ya'yan kungiyar tare da biyan diyya na asarar da ta faru ga mutanen da rikicin ya shafa a jihohin Benue da Taraba.
A taron manema labarai da kungiyar ta kira da marecen wannan Lahadi a birnin Abuja, kungiyar ta nisanta kanta da kokarin da ta ce ana yi na ba ta mata suna a matsayin kungiyar ‘yan tada a Najeriya.