Najeriya da ECOWAS za su yaki bazuwar makamai | BATUTUWA | DW | 16.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Najeriya da ECOWAS za su yaki bazuwar makamai

A kokarin Najeriya na shawo kan matsalar yaduwar makamai a hannun jama'a da ke da alaka da kashe-kashen rayuka a kasar, gwamnati ta fara wani aiki da kungiyar ECOWAS don dakile shigar makamai cikin kasar.

Taron shugabannin ECOWAS kan maganta matsalar tsaro

Taron shugabannin ECOWAS don neman hanyoyin maganta matsalar tsaro

Bazuwar kananan makamai tsakanin al'ummar Najeriyar da sannu a hankali mallakar bindigogi ke kara yawaita saboda shigo da su da ake yi ta barauniyar hanya daga kasashe makwabta musamman ma dai kasar Libiya, shi ne ya tayar da hankalin Najeriya da ya sanya ma'aikatar kula da harkokin cikin gidan kasar tunkarar kungiyar kasashen Afirka ta yamma ta ECOWAS domin su yi aiki tare.

Russland Waffe Kalaschnikow-Modell AK-47 (picture-alliance/dpa)

Daya daga cikin makaman da ake ta'adi da su

Wannan matsala da a yanzu ake ganinta a zahiri, inda ake amfani da wadannan bindigogi ta hanyar fataucin miyagun kwayoyi da ma masu fasa-kwaurin sigari, wadanda ke amfani da kudadden wajen daukar nauyin harkokin ta'adanci, matsalar da shekaru biyar kenan Najeriya ke fafatawa da ita. Kungiyar Ecowas dai ta kafa wani kwamiti mai karfi da gwamnatin Najeriya domin shawo kan matsalar da ta sanya munin rigingimu tsakanin Fulani da manoma sakamakon watsuwar makaman.

Kindersoldaten Jugendlicher mit einer AK-47 Uganda Sudan Lord's Resistance Army LRA (Getty Images/S.Price)

Wani dan bindiga dadi da AK 47

Koda yake bisa yarjejeniyar ta ECOWAS an amince da zirga-zirga da dabbobi ga makiyaya a kasashen kungiyar, amma shugaban kungiyar Marcel Alain de Souza, ya ce dole ne ECOWAS din ta dau kwararan matakai a kan wannan matsala.

 

Ya ce  ‘'ai muna da yarjejeniyar zirga-zirga, amma ba a mutunta ne kawai shi ne ya sa daukacin kasashen wannan kungiya, muke da matsala ta watsuwar makamai, kuma matsalar ita ce duk da an samar da burtali na makiyaya ba su bin inda aka shata, sannan ga manoma sun cinye mafi yawan wuraren, don haka dole mu dauki matakin mutunta wannan yarjejeniya.

Za a sa ido a ga dubarun da Ecowas din da Najeriya zasu bullo da su a taron koli da za su yi a wata mai zuwa a kan wannan matsala da ta zama tamkar wutar daji a kasashe 15 na kungiyar.

 

Sauti da bidiyo akan labarin