Najeriya: Gwamnan Filato ya soki dokar hana kiwo | BATUTUWA | DW | 11.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Najeriya: Gwamnan Filato ya soki dokar hana kiwo

A wani mataki na nuna sabani kan batun rikin manoma da makiyaya a Najeriya, gwamnan jihar Filato Simon Lalong ya soki matakin gwamnonin Benue da Taraba na kafa dokar hana kiwo ba tare da yin adalci ba.

Nigeria Konflikt Farmer Pastoralisten (DW/K. Gänsler)

Kiwo na makiyaya na haddasa tashin hankali a wasu jihohin Najeriya

Har ya zuwa yanzu dai ana kirga asara a lunguna da sakuna na tsakiyar Tarrayar Najeriya, har kuma yanzu zuciya tana numfasawa a game da rikicin makiyaya da manoman da ke neman rikidewa ya zuwa na siyasa. To sai dai kuma har a tsakanin shugabannin yankin da wannan rikici ya fi kamari ana kara samun rabuwar kawuna game da dokar hana kiwon da ke zaman musabbabin rikicin da ke kara tada hankali. Gwamnan jihar Filato Simon Lalong ya ce ba hujjar kafa dokar tun da farkon fari ba tare da tabbatar da samar da hanyoyi na aiwatar da ita.

Flash-Galerie Tuareg (AP)

Makiyaya masu kiwon shanu na fuskantar kalubale

Gaggawa a cikin mulkin jama'a ko kuma kokari na cika buri a siyasa dai,  a yayin da ake kirga asara a jihohin na Benue da Taraba dai an kamalla bukukuwan kirisimeti da na sabuwar shekara lafiya da kwanciya ta hankali a jihar Filato da a baya take zaman cibiyar rigingimu makamantan wannan. To sai dai kuma  babban sirrin a fadar Gwamna Lalong na zaman rungumar daukacin al'umma ta Filato a cikin halin adalci a tsakanin kowa. Ana dai kallon sabon rikicin da ya dauki launi irin na banbancin kabila da kila ma na addini a cikin yankin ka iya rikidewa ya zuwa na siaysa ga kasar da ke kara tunkarar lokaci na zabuka.

Sauti da bidiyo akan labarin