RAHOTANNI SUN TABBATAR DA CEWA YAKIN KASAR IRAQI BA KARAMAR ILLA YAYIWA KASASHEN NAHIYAR TURAI BA;MUSANMAMMA TA HANYAR BARAKA DA AKA SAMU A TSAKANIN SU...IBRAHIM SANI.... | Siyasa | DW | 18.03.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

RAHOTANNI SUN TABBATAR DA CEWA YAKIN KASAR IRAQI BA KARAMAR ILLA YAYIWA KASASHEN NAHIYAR TURAI BA;MUSANMAMMA TA HANYAR BARAKA DA AKA SAMU A TSAKANIN SU...IBRAHIM SANI....

KWAMISHINONIN HUKUMAR ZARTARWA NA KUNGIYYAR EU A TSAYE TARE DA SHUGABAN SU A TSAKIYA MR ROMANO PRODI.

default

Nasarar da Jamiyyar socialist ta kasar Spain ta samu a zaben faraministan kasar na kwanakin baya,a yanzu haka ya zamanto wata katanga ta dinke barakar dake akwai a tsakanin wasu daga cikin kasashen nahiyar Turai.

Hakan a cewar rahotanni zai kuma karawa kasashen musanmamma na Jamus da Faransa kwarin gwiwar magana da yawu gudu a al,amurran siyasar yau da kullum.

Rahotanni dai a baya sun tabbatar da cewa an samu rashin fahimtar juna a tsakanin manya manyan kasashen biyu da kuma kasar Amurka musanmamma a kann yakin kasar iraqi.

Wan nan mataki dai da kasar ta Amurka ta dauka babu shakka a cewar rahotanni ya raba kawuwan kasashen nahiyar ta Turai,a misali kasashe irin su Biritaniya da spain da Italiya da Poland da Denmark a wancan lokaci na marawa kasar ta Amurka baya ne na kaiwa iraqi harin na soji.

A hannu daya kuma kasashe irin su Jamus da Faransa suka hau kujerar nakin shiga tawagar kaiwa iraqin harin na soji.

Kasancewar wan nan al,amari ya haifar sakataren tsaro na Amurka Donal Rumsfeld na cewa kasashen na Jamus da Faransa na a matsayin tsohuwar nahiyar ta turai ne,sabbin kasashe dake cikin nahiyar ta Turai kuma sune kasashe dake marawa kasar ta Amurka baya na kaiwa iraqi harin na soji.

Bugu da kari a wancan lokaci bayanai sun shaidar da cewa an gaza samun daidaituwa a tsakanin kasashen na nahiyar ta Turai bisa wan nan batu na yakin kasar ta iraqi.

To amma a halin yanzu sakamakon lashe zaben Jose Luis Rodriguez a matsayin sabon faraministan kasar Spain,a karkashin jamiyyar Socialist,alamu na nuni da cewa hakan zai taimakawa nahiyar ta turai ta bude wani sabon babi na cimma daidaito wajen magana da murya daya.

A misali a cikin jawabin sa na farko bayan samun nasara,Mr Zapareto ya fadawa yan jaridu cewa yakin kasar iraqi babu abin da ya haifar illa annoba,adon haka ya bukaci shugaban Amurka da kawayen sa dasu dinga yin karatun mun natsu kafin daukar mataki na karshe a abubuwa irin wadan nan daya shafi biliyoyin al,ummar duniya.

Bisa ire iren furuce furucen sabon faraministan game da sukar lamirin yakin na iraqi,itama kasar Faransa ta hanyar ministan harkokin wajen ta Dominique De Villepin a ranar litinin data gabata ya kara sukar lamirin kasashen da suka kaiwa kasar ta Iraqi harin na soji da cewa abune dake a matsayin babban kuskure.

Ministan harkokin wajen kasar ta Faransa yaci gaba da cewa yakin kasar iraqi a yanzu haka ya haifar da dan da bashi da ido,na rashin zaman lafiya a kasar tare da ci gaba da kyankyasar yan taadda a doron kasa baki daya.

Dominique De Villepin ya kara da cewa hanya ta farko ta kyankyasar yan taadda ta fito ne daga yankin gabas ta tsakiya,sakamakon mamaye da kasar Bani israela tayiwa yankin Palasdinawa,hanya ta biyu kuma a cewar sa itace sakamakon yakin kasar iraqi.

A waje daya kuma shima shugaban hukumar zartarwa na kungiyyar tarayyar Turai,Romano Prodi ya soki lamirin kasar ta Amurka bisa jagorancin yakin kasar na iraqi,da cewa shekara daya baya aiyukan yan taadda bashi da karfi da kuma yawa kamar a yanzu.

A dai shekarun baya kadan kasashen na nahiyar turai sun gaza cimma mataki daya kann batutuwa da suka shafi matakan harkokin waje da kuma tsaro,kuma ba komai ne ya janyo hakan ba illa rarrabuwar kai ne da aka samu lokacin yakin kasar iraqi.

To amma a yanzu haka abubuwa sun fara dai daita musanmamma na juyin gwamnati da aka fara samu a kasar Spain.