1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa na son a karfafa tsaron Turai

Lateefa Mustapha Ja'afar
February 17, 2023

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya bukaci kasashen Turai da su kara zuba hannun jari a kan harkokin tsaro, yana mai cewa in har Turai na son zaman lafiya tilas ta zage damtse a fannin tsaro.

https://p.dw.com/p/4Nfnl
Emmanuel Macron l Faransa | Taro | Munich | Tsaro | Turai
Shugaban kasar Faransa Emmanuel MacronHoto: Odd Andersen/AFP via Getty Images

Shugaba Emmanuel Macron na Faransan ya bayyana hakan ne, a jawabin da ya yi a wajen taron tsaro na duniya da ke gudana a yanzu haka a birnin Munich na Jamus. A cewarsa yana fata nan da lokacin bazara da ke tafe, za a cimma wata gagarumar matsaya kan batun na tsaro domin in har Turai na son kare kanta tilas ta sama wa kanta makamai. Taron da ke zuwa gab da cika shekara guda da mamaye Ukraine da Rasha ta yi, ya sanya Amurka da kasashen Turan sake kakabawa Shugaba Vladmir Putin na Rasha karin takunkumi. A hannu guda kuma, ministan tsaron Jamus Boris Pistorius ya bayyana cewa Turai din fa ba kanwar lasa ba ce kamar yadda Putin ke tunanin ta gaza katabus.