Majalisar Dinkin Duniya ta ce Sudan na bukatar taimakon dola miliyan 40 ga manomanta. | Labarai | DW | 30.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar Dinkin Duniya ta ce Sudan na bukatar taimakon dola miliyan 40 ga manomanta.

Hukumar Aikin Noma Da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya, wato FAO a takaice, ta ce kasar Sudan na bukatar kimanin dola miliyan 40 a wannan shekarar don tallafa wa fannin nomanta, wanda kusan kashi 90 cikin dari na al’umman kasar suka dogara a kansa. Hukumar ta kara da cewa, z ata yi iyakacin kokarinta a wannan shekarar, wajen tallafa wa kusan mutane miliyan 5 da digo 5, `yan kasar Sudan din, wadanda suka dogara kacokan kan noma don iya tafiyad da halin rayuwarsu. Ta kuma dai yi kira ga kasashe mawadata, da su ba da tasu gudummuwa don cim ma wannan manufar.

A cikin wata sanarwar da Hukumar ta bayar yau a birnin Khartoum, shugaban reshenta na ba da taimakon agaji na gaggawa, Anne Breuer, ta bayyana cewa dimbin yawan shekarun da aka shafe cikin wani hali na tabarbarewar tsaro a kasar sun janyo matsaloli da dama ga halin rayuwar jama’a, da habaka yawan talauci, abin da kuma ya janyo yunwa da dai sauransu ga mafi yawan al’umman kasar.