Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce Isra’ila ta take ƙudurin tsagaita buɗe wuta da harin da ta kai a Lebanon. | Labarai | DW | 20.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce Isra’ila ta take ƙudurin tsagaita buɗe wuta da harin da ta kai a Lebanon.

Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Kofi Annan ya yi watsi da uzurin da Isra’ila ta bayar na cewa harin da sojojin ƙundumbalanta suka kai a Lebanon, don kare kanta ne, kuma ya ce wannan matakin dai ya zo daidai da take ƙudurin tsagaita buɗe wutan da kwamitin sulhu na majalisar ya cim ma a farkon wannan makon.

A cikin wata sanarwar da Majalisar Ɗinkin Duniyar ta buga a birnin New York, Kofi Annan ya bayyana matuƙar damuwarsa ga harin da dakarun Isra’ilan suka kai a gabashin Lebanon, wanda ya ce wata makarkashiya ce ga gwamnatin ƙasar. Ya nanata cewa, matakin Isra’ilan zai iya taɓarɓare al’amura bayan cim ma kwantad da ƙurar rikicin da aka yi.

Jami’an sa ido na Majalisar Ɗinkin Duniya a yankin dai sun ba da rahotanni da dama na saɓa wa ƙudurin tsagaita buɗe wutar da jiragen saman yaƙin Isra’ilan suka yi. Amma ita Isra’ilan da kanta, ta ce ta kai harin ne don hana ’yan kungiyar Hizbullahi yin jigilar makaman da suka samu daga Iran ta kan Siriya, zuwa bakin daga.