1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin Larabawa kan yarjejeniyar Iran

Salissou Boukari
May 9, 2018

Kungiyar kasashen Larabawa ta yi kira da a sake tattauna yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran kwana daya bayan da shugaban Amirka Donald Trump ya sanar da matakin janye kasarsa daga yarjejeniyar.

https://p.dw.com/p/2xRv9
Saudi-Arabien Gipfel Arabische Liga in Dhahran
Hoto: Getty Images/AFP

A ranar Talata ce dai Shugaba Donald Trump ya sanar da matakin fitar da Amirka daga yarjejeniyar nukiliyar kasar ta Iran duk kuwa da lallashin da wasu kasashe kawayen kasar ta Amirka suka yi masa.  A watan Yuli ne di na 2015 a birnin Vienna kasashen China, Amirka, Faransa, Britaniya Rasha da Jamus suka kulla yarjejeniya kan batun nukiliyar kasar ta Iran tare da da Iran din.

Da yake magana daga cibiyar kungiyar da ke a birnin Alkahira, Sakatare Janar na kungiyar kasashen Larabawan Ahmed Aboul Gheit, ya ce ya zama wajibi a sake tattauna yarjejeniyar nukiliyar kasar ta Iran, inda ya nuna damuwar kasashen na larabawa da abun da ya kira tsagerancin kasar Iran a yankin.

Kasar Saudiyya da ke a matsayin babbar mai adawa da kasar Iran, kuma babbar kawa ga Amirka, ta yaba tun a ranar ta Talata da matakin da shugaban Amirka Donald Trump ya dauka na ficewa daga yarjejeniyar nukiliyar kasar ta Iran.