Saudiyya na da yawan al'umma da suka kai miliyan 30 kuma gidan sarautar kasar ne ke mulkar wadannan mutane.
Kasar na daga cikin kasashen duniya da ke da dumbin arziki, musamman ma na albarkatun man fetur da iskar gas. 'Yan gidan saurautar kasar na bin tafarkin Sunna ne kuma kasar ita ce ta biyu da ke kan gaba wajen sayen makamai a duniya.