Kotu a Jamus ta daure wani dan fashin teku | Labarai | DW | 17.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotu a Jamus ta daure wani dan fashin teku

Wata kotun Jamus ta yanke hukuncin daurin shekaru 12 ga wani dan Somaliya da ta samu da laifi na fashin teku da aka yi kimanin shekaru hudun da suka gabata.

Mutumin wanda kotun ba ta bayyana sunansa ba na daga cikin wanda suka jagoranci fashin jirgin da yin garkuwa da wadanda ke cikinsa har ma suka azabtar da su na tsawo wattani takwas, kafin daga bisani su sako su bayan da kamfanin jirgin ruwan ya biya kudin fansa har euro miliyan uku da rabi.

A cikin shekarar da ta gabata ce dai aka kama mutumin dan shekaru 44 da haihuwa yayin da ake tanance zanen yatsunsa na hannu daidai lokacin da ya yi amfani da takardun bogi wajen neman mafaka irin ta 'yan gudun hijira a nan Jamus.

Kotun dai ta bashi mako guda na ya daukaka kara idan har bai amince da hukuncin ba.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammed Awal Balarabe