Jamus za ta shiga cikin aikin lalata makamai masu guba na Siriya | Labarai | DW | 09.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus za ta shiga cikin aikin lalata makamai masu guba na Siriya

Kasar Jamus dai na da cikakkiyar kwarewa a aikin kawar da makamai masu guba, saboda haka ta yanke shawarar ba da tata gudunmawa.

Ministan harkokin wajen Tarayyar Jamus Frank-Walter Steinmeier ya ce kasarsa za ta shiga cikin aikin lalata makamai masu guba a Siriya. Ministan ya fada a birnin Berlin cewa bai kamata Jamus mai kwarewar fasaha a wannan fannin ta ki shiga cikin wannan aiki ba. Saboda haka gwamnatin tarayya ta yanke shawarar kawar da birbishin sinadaran makaman a barikin rundunar sojin kasar dake garin Munster na jihar Lower Saxony. Ya ce za su yi wannan aiki ne bayan kwararru daga kasar Amirka sun yi daya-daya da makaman masu guba. Kudurin Majalisar Dinkin Duniya dai ya tanadi da a kammala lalata makaman gubar na Siriya kafin tsakiyar wannan shekara da muke ciki.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu