Jamus ta bukaci Rasha ta guji matsawa kungiyoyin fararen hula
April 8, 2013Talla
Uwargida Merkel ta yi wannan kiran ne a birnin Hannover na nan tarayyar Jamus inda shugabannin biyu ke hallarta kasuwar baje kolin sabbin kayakin lantarki da intanet da kuma na masana'antu da aka saba yi a kowace shekara.
Wannan kiran na Merkel dai ya biyo bayan irin afkawar da gwamnatin Rasha ta ke yi wa ofisoshin kungiyoyin da ba na gwamnati ba a dan tsakanin nan to sai dai Rasha ta nace cewar wannan mataki da ta kan dauka ba wai da nufin gallazawa jama'a ba ne, sai dai don sanya idanu kan wasu 'yan kasahen wajen da ke kokarin amfani da 'yan adawa wajen tada zaune tsaye a kasar.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Yahouza Sadissou Madobi