Jam´iyar PDP a Nijeriya ta zabi Umar ´Yar´aduwa a matsayin dan takararta | Labarai | DW | 17.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jam´iyar PDP a Nijeriya ta zabi Umar ´Yar´aduwa a matsayin dan takararta

Gwamnan jihar Katsina dake arewacin Nijeriya, Alhaji Umar ´Yar´aduwa yayi nasarar lashe zaben fid da dan takarar shugaban kasa a karkashin tutar jam´iyar PDP a zaben shugaban tarayyar Nijeriya da za´a yi a cikin watan afrilun shekara mai zuwa. Wata sanarwa da jam´iyar ta PDP mai jan ragamar mulki a Nijeriya ta bayar dazu-dazun nan bayan ta kammala babban taron ta a Abuja, ta nunar da cewa Umar ´Yar´aduwa ya lashe zaben a matsayin wanda zai gaji shugaba Olusegun Obasanjo a mukamin shugaban Nijeriya, kasar da ta fi kowace kasar Afirka yawan al´uma. ´Yar´aduwa mai shekaru 55 kuma tsohon malamin makaranta ya lashe zaben fid da dan takarar da gagarumin rinjaye na kimanin kuri´u dubu 4, to sai dai bisa ga dukkan alamu zai fuskanci kalubale daga jam´iyun adawa a zaben shugaban kasar a watan afrilu.