PDP ta kasance jam'iyyar da ta karbi madafun ikon Najeriya a shekarar 1999 lokacin da kasar ta koma tafarkin demokaradiyya.
Jam'iyyar ta sha kaye a zaben shekara ta 2015 bayan mulkin shekaru 16. PDP ta taka muhimmiyar rawa a fannoni rayuwa daban-daban na Najeriya kuma ta fuskanci bore daga wasu mambobin jam'iyyar abin da ya taimaka aka kayar da ita a zaben shekara ta 2015.