1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Alkiblar da APC ta dosa a Najeriya

August 21, 2013

Babbar jam'iyyar adawa ta APC ta gudanar da babban taronta na farko inda ta gabatar da muhimman manufofinta guda takwas.

https://p.dw.com/p/19UKX
Hoto: AP

Kadammar da manufofi takwas ga babbar jam'iyyar adawar ta APC na zama tamkar aza harsashi ne da ma share fagen inda jam'iyyar ta dosa a guguwar siyasar Najeriyar da ke ci gaba da kadawa domin shirye-shiryen zaben shekara ta 2015.

Shugabanin jam'iyyar sun tabo halin da Najeriya ke ciki da suka hada da batun rashin tsaro da cin hanci da rashawa da koma bayan ingancin rayuwar al'umma musamman ma dai talakawa.

Wannan taron dai shi ne na farko tun bayan samun rijistarsu da ke sauya yadda iskar siyasar Najeriyar ke kadawa, to ko wane babbanci akwai a tsakanin wadanan manufofi da na jam'iyyun da APC kewa kalon hadarin kaji? Malam Nasiru Nasiru E-Rufai shi ne mai rikon mukamin mataimakin sakatataren na wanan jamiyyar, ya ce ai bambancin a fayyace ya ke.

Plakat Nigeria Präsidentenwahlkampf
Jam'iyyar PDP za ta zamewa APC karfen kafa a 2015Hoto: DW/U.Haussa

''Rashin lafiya ne matsala ta farko da ke damun Najeriya kuma gwamnatin APC za ta tabbatar da cewa mutanen Najeriya sun zauna lafiya. Akwai mutane miliyan 170 a Najeriya wanda rabinsu matasa ne, basu da aikin yi, jamiyyar APC zata kawo gyara a kan wannan. Kazalika za ta yi gyara yadda manomi zai samu taki yayin da masu masana'antu zasu samu lantarki. Da haka ne za'a samar da ayyuka''

Batun kasancewar gwamnan jihar Imo na jamiyyar APGA a cikin wanan tafiya ya zamo abinda ke sanya tada jijiyar wuya saboda matsayin da uwar jamiyyarsa ta dauka na nisanta kanta da matakin da ya dauka har ma da barazanar za su nufi kotu, wannan ya sanya tambayar gwamanan na jihar Imo shin ina aka kwana ne a kan wanan batu?

''APC dai ai tamu ce yanzu ba mai maganar APGA, don in ka duba zaka ga ya kamata a ce sashin kudu maso gabashin Najeriya muna cikin jamiyyar APC domin akwai arewa da kuma yankin kabilar Yarabawa to ya kamata mu ma muna cikin jamiyyar APC. Dalili kuwa shi ne ana neman hanyar da za a fitar da mutane saboda haka ya kamata muna APC don a taimaki jama'a''

Nigeria Präsident Goodluck Jonathan Beerdigung Autor Chinua Achebe OVERLAY GEEIGNET
Idan PDP ta tsayar da Jonathan wa zai kalubalance shi a APCHoto: Pius Utomi ekpei/AFP/Getty Images

Duk da doki da murnar da 'ya'yan jamiyyar ke yi da har suka sanar da Dr. Chris Ngige a matsayin dan takarara jamiyyar a zaben jihar Anambra da za a yi nan gaba a Najeriyar, hankulan wasu 'ya'yan jam'iyyar ya karkata ga rikicin cikin gida da ya kuno kai. Sanata Kabiru Gaya jigo a jamiyyar ya ce akwai bukatar sanin inda aka dosa game da wannan batu.

''In ka duba tarihin baya APP ce ta hadu saboda haka tafiya ce da ake neman hadin kai, don haka sai a yi hakuri da duk wani jayaya a zo a tafi baki daya''

Da alamun dai za a fafata a fagen siaysar Najeriyar domin kuwa jam'iyyar ta APC ta bayyana bukatar a bullo da amfani da hanyar tanatace zaben 'yar natsa na zamani wajen jefa kuri'a domin dakile makudi da masu dangwale a zabe, abinda kan jefa tababa a sahihancin zabubbukan kasar.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Mouhamadou Awal