1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afghanistan ta zargi kasashen duniya da gazawa a yaki da ta´addanci

September 2, 2006
https://p.dw.com/p/Bukq

Shekaru biyar bayan kaddamar da yaki da ´yan ta´adda, gwamnatin Afghanistan ta zargi gamaiyar kasa da kasa da gazawa. Ministan harkokin waje rangin Dadfra Spanta ya fadawa kamfanin dillancin labarun Jamus a birnin Kabul cewa kusan dukkan taimakon da ake ba wa Afghanistan ya ta´allaka akan aikin soji. Ya ce yaki da ta´ddanci ya kunshi ba da taimakon raya kasa da kuma aikin kyautata jin dadin jama´a. Ministan ya kuma amsa cewar gwamnatinsa ta tabka kurai kurai a yakin da take da cin hanci da rashawa da manoman ganye mai sa maye da kuma ta´addanci. Yanzu haka dai masu fataucin miyagun kwayoyi da kuma ´yan ta´dda na bawa juna hadin kai. Mista Spanta ya ce idan ba´a hada hannu da karfe an yaki wadannan matsaloli a lokaci daya ba, to ba za´a samu wata nasara ba.