Ziyarar Shugaban Jamus a Najeriya | Siyasa | DW | 11.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ziyarar Shugaban Jamus a Najeriya

Yayin wannan ziyarar dai shugaban tarayyar Jamus Joachim Gauck ya gana da marubutan litattafan adabi da jagororin addini kana ya kai ziyara sansanin 'yan gudun hijira da ke Abuja.

A matakin da ke nuna kara yaukaka dangantaka tsakanin Najeriya da kasar Jamus, shugaban kasar Jamus din Joachim Gauck ya kai wata ziyarar kwanaki hudu a tarayyar Nijeriya. Ziyarar shugaban kasar Jamus din na zuwa ne a dai-dai lokacin da Najeriya ke fuskantar kalubale mai yawa kama daga tattalin arziki zuwa ga tsaro da ma na yanayin zamantakewar al'ummarta.

DW.COM

Sauti da bidiyo akan labarin