Shugaban Jamus ya jinjinawa Najeriya kan zaben shekara ta 2015 | Labarai | DW | 09.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Jamus ya jinjinawa Najeriya kan zaben shekara ta 2015

A cigaba da ziyarar da yanzu haka yake a tarayyar Najeriya shugaban kasar Jamus Joachim Gauck ya jinjinawa kasar abisa nasarar gudanar da zaben shugaban kasa a shekara ta 2015.

Shugaban Jamus din yace Najeriya ta zama zakaran gwajin dafi a tsakanin kasashen Afrika. 

Shugaban tarayyar Jamus din dai na wadan nan kalaman ne a yayin da yake ganawa da fitaccen marubucin adabin nan Ferfesa Wole Soyinka a jihar lagos dake kudu maso yammacin Najeriya.

Joachim Gauck ya kuma jinjinawa kasar abisa yunkurin ta na kakkabe ayyukan Boko Haram a inda ya kara da cewa akwai bukar sake zage dantse domin yaki da ayyukan ta'addanci.

Ana sa ran dai zai gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar alhamis din nan a yunkurin sa na kara karfafa dangantaka tsakanin kasasen biyu tare da kai ziyarar gani da ido yankin arewa maso gabashin kasar da ayyukan Boko Haram ya shafa.