Shugaban Jamus Gauck na ziyara a Najeriya | Labarai | DW | 08.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Jamus Gauck na ziyara a Najeriya

Matsalar tsaro da harkar kasuwanci na daga cikin abubuwan da shugaban Jamus Joachim Gauck zai mayar da hankali a kai da takwaransa Buhari na Najeriya.

Shugaban tarayyar Jamus Joachim Gauck zai fara ziyarar aiki a wannan Litinin a tarayyar Najeriya bisa rufin bayan wata tawagar 'yan kasuwar kasarsa. Matsalar tsaro da ake fama da ita a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya sakamakon hare-haren Boko Haram, ta na sahun gaba da abubuwan da zai tattaunawa da hukumomin kasar.

Wasu masu sukar kamun ludayin shugaba Muhammadu Buhari sun bayyana cewar har yanzu gwamnatinsa, ta kasa murkushe tsagerun da ke kai hare-hare da sunan addini kamar yadda ya alkawarta a yakin neman zabe, saboda har yanzu suna addabar tarayyar ta Najeriya da kasashen da ke makwabtaka da ita.

Ziyarar ta Gauck ta zo ne a daidai lokacin da kungiyoyin kodago suke nuna fishinsu a Abuja da sauran sassa na Najeriya sakamakon karin farashin wutar lantarki.