Wata kotu a nan Jamus ta bada sanmaci kan ′yan tarzoma | Labarai | DW | 04.01.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wata kotu a nan Jamus ta bada sanmaci kan 'yan tarzoma

Wata kotun tarraya a nan Jamus ta bada sanmacin sake kamo wasu ‚yan tarzoma biyu na ƙungiyar RAF da aka saki bayan sun yi shekaru masu yawa suna zaman kurkuku. Kotun dake Karslsruhe a yankin kudu-maso yanmacin Jamus, tace zata tilastawa Brigitte Manhaupt da Knut Folkerts su bayyana sunan wani da ake zarginsa da kisan babban alƙali da wasu mutane biyu nan yanmacin Jamus a shekara ta 1997. Kana alƙalin kotun ya buƙaci, Christien Klar da ke tsare a gidan kurkuku yanzu haka, da ya fuskanci tambayoyi game da wannan kisan. Mutanen uku zasu fuskanci hukumcin daurin shekaru ko kuma tarar diya idan suka ƙi bada haɗin kai.