Tarihin ranar ma′aikata ta duniya | Amsoshin takardunku | DW | 08.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Tarihin ranar ma'aikata ta duniya

Ita dai ranar ma'aikata ta duniya wadda ake wa lakabi da International Workers' Day ta samo asalinta ne kimanin shekaru 140 da suka wuce wato 4 ga watan Mayun shekarar 1888.

Ita dai ranar ma'aikata ta duniya wadda ake wa lakabi da International Workers' Day ta samo asalinta ne kimanin shekaru 140 da suka wuce, wato ranar 4 ga watan Mayun shekara ta 1888 lokacin da wasu ma'aikata da jami'an tsaro suka yi taho mu gama a birnin Chicago na Amirka yayin da ma'aikatan ke zanga-zanga dangane da yawan sa'o'in da ma'aikaci ya yi a bakin aiki.

Wannan tashin hankali dai ya yi sanadiyyar rasuwar mutane da dama tare da jikkata wasu, lamarin da ya sanya bayan wani dan lokacin kasashe musamman ma dai na yammacin duniya suka kebe wannan rana domin tuwanawa da wadanda suka rasu a Chicago din ranar 4 ga watan Mayun shekara ta 1888, sai dai an maida bikin ne zuwa ranar farko ta watan Mayun kowacce shekera.

Faransa ce dai ta fara bikin tunawa da zagayowar wannan rana da ma'aikata suka hallaka sakamakon rikicin da suka yi da jami'an tsaro, inda a shekarar ta 1899 aka yi gagarumin gangami

Shi dai wannan bikin ana yinsa ne a kimanin kasashe tamanin na duniya kuma ya na gudana ne a rana daya wato daya ga watan Mayun kowacce shekara, sai dai ya banbanta da kasa zuwa kasa idan akan yi la'akari da sanda aka fara gudanar da shi a kowacce kasa.

Nahiyar Afirka ma dai ba za a ce ta zama kurar baya domin kasashenta na gudanar da shi sai dai akan dan samu banbanci dangane da irin abubuwan da ake gudanar. Yawanci a kasashe irin su Najeriya ma'aikata kan hadu a wajen guda tare da shugabannin kungiyoyin kwadago don yi jawabi da mika korafin ma'aikata ga mahukunta.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammad Nasiru Awal