Majalisar Dinkin Duniya ta janye kananan ma´aikatanta daga Timor Ta Gabas | Labarai | DW | 27.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar Dinkin Duniya ta janye kananan ma´aikatanta daga Timor Ta Gabas

A dangane da tashe tashen hankula a Timor Ta Gabas, MDD ta fara kwashe kananan jami´anta daga yankin zuwa Australiya. Majalisar zata bar ma´aikata 50 daga cikin 440 da take da su a Timor Ta Gabas. A ´yan kwanakin nan dai an yi ta arangama tsakanin sojoji masu biyayya da gwamnati da kuma wadanda aka sallame su daga aikin soji bayan sun shiga cikin wani yajin aiki. A kuma halin da ake ciki tashe tashen hankulan sun bazu a tsakanin kungiyoyin matasa wadanda ba sa ga maciji da juna. A halin da ake ciki dubban mazauna Dili babban birnin kasar sun tsere zuwa filin jirgin saman birnin dake karkashin kulawar sojojin Australiya.