Kungiyar EU ta yi kira da a gudanar da zabe na adalci a Kongo | Labarai | DW | 29.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar EU ta yi kira da a gudanar da zabe na adalci a Kongo

KTT ta bi sahun MDD wajen yin kira ga al´umar kasar ta Kogo da su fita kwansu da kwarkwatansu wajen kada kuri´a a zaben na gobe lahadi. Wata sanarwar da kungiyar ta EU ta bayar ta nunar da cewa bayan shekaru fiye da 40 yanzu ´yan Kongon sun samu damar zabarwa kansu shugabanni ta hanyar demukiradiya. Kakakin rundunar EU a Kongo Peter Fuss ya ce sun kammala dukkan shirye shiryen kula da yadda zaben zai gudana. Sama da mutane miliyan 25 ake kwwautata zato zasu kada kuri´a a zabukan na shugaban kasa da na ´yan majalisun dokokin a Kongo.