1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Scholz: Gujewa ta'azzarar al'amura a Gaza

Lateefa Mustapha Ja'afar
April 21, 2024

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya bukaci Isra'ila da ta guji kara ta'azzarar al'amura a yankin Gabas ta Tsakiya, a daidai lokacin da ake ci gaba da gwabza yaki tsakaninta da kungiyar Hamas.

https://p.dw.com/p/4f1zn
Jamus | Berlin | Shugaban gwamnati | Olaf Scholz | Gabas ta Tsakiya
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf ScholzHoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

Shugaban gwamnatin Jamus din Olaf Scholz ya yi wannan kiran ne, yayin wata tattaunawa da ya yi da firaministan Isra'ilan Benjamin Netanyahu ta wayar tarho. A hannu guda kuma, Scholz ya yi karin haske kan kudirin shugabannin kasashe mambobin kungiyar Tarayyar Turai EU na kakaba sabon takunkumi a kan Iran. A cewarsa Jamus za ta bayar da hadin kai da goyon baya ga takwarorinta na EU da kuma na kungiyar Kasashe masu Karfin Tattalin Arziki na Duniya wato G7, wajen kakaba karin takunkumin karya tattalin arziki ga Tehran.