Falasdinu na da matsayin 'yar kallo a Majalisar Dinkin Duniya. A tarihance kasa ce mai tsarki da Yahudawa da Kiristoci da Musulmi da ke samun sabani a kanta.
Yakin ya kunshi zirin Gaza da yankunan da ke yamma da kogin Jordan. Falasdinawa na adawa da mamaye wasu yankunansu da Isra'ila ta yi bayan da aka kafata a 1948.