Isra'ila kasa ce da ke yankin Gabas ta Tsakiya. Kasar na da iyaka da tekun Bahar Rum kuma an girka ta ne a cikin shekara ta 1948.
Isra'ila ita kadai ce daga cikin jerin kasashen duniya da galibin al'ummarta Yahudawa ne. Kasar na daukar Birnin Kudus a matsayin babban birninta sai dai Majalisar Dinkin Duniya ba ta amince da hakan ba. Tel Aviv ita ce cibiyar kasuwancin kasar. Isra'ila na rikici da Falasdinawa kan mallakin Zirin Gaza.