1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Masu zanga-zanga a Amurka sun kona tutar kasar

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 25, 2024

Mataimakiyar shugaban kasar Amurka kana 'yar takarar shugaban kasa a jam'iyyar Democrats mai mulki Kamala Harris ta yi tir da abin da ta kira wauta, wadda masu zanga-zangar nuna goyon bayan Falasdinawa suka nuna.

https://p.dw.com/p/4ikH6
Amurka | Washington | Zanga-Zanga | Goyon Baya | Falasdinawa | Benjamin Netanjahu
Zanga-zangar goyon Falasdinawa, a lokacin firaministan Isra'ila ke ziyara a AmurkaHoto: Nathan Howard/REUTERS

Mataimakiyar shugaban kasar Amurka kana 'yar takarar shugaban kasa a jam'iyyar Democrats mai mulki Kamala Harris ta bayyana hakan ne, sakamakon kona tutocin Amurkan da masu zanga-zangar nuna goyon bayan Falasdinawana suka yi gabanin ziyarar firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu. Ana dai sa ran Firaminista Netanyahu na Isra'ilan zai kai ziyarar da aka jima ana dako zuwa fadar gwamnatin Amurka ta White House, inda zai gana da shugaban kasar Amurkan Joe Biden kana ana sa ran zai gana da 'yar takarar shugaban kasar ta jam'iyyar Democratic kana mataimakiyar shugaban kasa Kamala Harris yayin ganawar da ke da muhimmanci ga 'yan siyasar uku.