G7 kungiya ce ta kasashen da ke kan gaba wajen karfin masana'antu a duniya. A cikin shekara ta 1975 ne aka kafa wannan kungiya.
Kasashen da suka hada da Burtaniya da Jamus da Amirka da Faransa da Italiya da Japan da kuma Kanada. A shekara ta 1998 ne aka sanya Rasha a kungiyar wanda hakan ya sa aka sauya mata suna G8, sai dai daga baya an cire Rashan bayan da ta mamaye yankin nan na Kirimiya.