1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha za ta fuskanci sabon matakin G7

Lateefa Mustapha Ja'afar
May 18, 2023

Akwai yiwuwar Rasha ta sake fuskantar wani salon takunkumin tattalin arziki daga kasashe masu karfin arzikin masna'antu na G7, a bangaren ma'adanin lu'u-lu'un da take da arzikinsa.

https://p.dw.com/p/4RYGI
Japan | G7 | Taro
Taron G7 na bana, Japan za ta karbi bakunciHoto: Issei Kato/REUTERS

Cinikin biliyoyin dalolin Amurkan na danyan lu'u-lu'u da Rashan ke da shi, kasashen na G7 na son su dakile shi ne a wani mataki na hukunta Moscow kan yakin da ta kaddamar a makwabciyarta Ukraine. Jakadun kasashen da dama sun shaidawa kamfanin dillancin labaran Jamus dpa cewa, daukar wannan matakin zai kassara kudin shiga da Rasha ke samu da kuma zai iya rage karfin da take da shi na yin yaki. Albarkatun lu'u-lu'u dai na daga cikin manyan hanyoyin samun kudin shiga na Moscow, baya ga albarkatun man fetur da iskar gas. Ana sa ran kasashen na G7 masu karfin arzikin masana'antu na duniya da suka hadar da Amurka da Jamus da Faransa da Italiya da Birtaniya da Kanada da kuma Japan, za su amince da wannan kudiri yayin taronsu da za su gudanar a birnin Hiroshima na kasar Japan.