Japan kasa ce da ke nahiyar Asiya kuma tana daya daga cikin kasashen da ke da karfin tattalin arziki ba wai a Asiya ba har ma a duniya baki daya.
Kasar na da yawan mutane da suka kai miliyan 126 wanda hakan ya sanya ta a matsayi na goma a jerin kasashen da ke da yawan al'umma. A shekarun da suka gabata kasar ta gamu da ibtila'in girgizar kasa da igiyar ruwan Tsunami wadda suka shafi cibiyar nukiliyarta ta Fukushima, wanda hakan ya haifar da asarar rayuka.