Jamus ta rufe ofishin jakadancinta a Kabul | Labarai | DW | 18.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus ta rufe ofishin jakadancinta a Kabul

Jamus ta ce ta rufe ofishin jakadancinta da ke birnin Kabul na kasar Afghanistan saboda rahotannin da ta samu cewar 'yan kungiyar nan ta Taliban na shirin kai masa hari.

Ein gepanzertes Fahrzeug von Typ Dingo steht am Donnerstag (14.06.2012) vor der Deutschen Botschaft in Kabul in Afghanistan. Foto: Michael Kappeler dpa

Ofishin jakadancin Jamus a birnin Kabul na kasar Afghanistan

Ministan tsaron tarayyar ta Jamus Thomas de Maiziere ne ya bayyana hakan a wannan Juma'ar a birnin Berlin inda ya kara da cewar sun yi gaggawar yanke wannan hukunci ne saboda labarin da suka samu cewar shirye-shiryen kai harin sun yi nisa.

Shi kuwa mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Jamus din Martin Schaefer ya shaidawa kamfanin dillacin labari na Jamus na Dpa cewar Jamus din ta yanke hukuncin rufe ofishin nata na jakadanci a Kabul din ne domin ta kare 'yan kasarta daga duka wani hari na ta'addanci.

Yanzu haka dai an dakatar da duk wani aiki a ofishin kamar dai yadda jaridar Die Welt da ake bugawa a nan Jamus ta shaida a daren jiya Alhamis.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammed Awal Balarabe