Jamus ta nemi a sako jami′an OSCE | Labarai | DW | 28.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus ta nemi a sako jami'an OSCE

Jamus ta nemi Rasha da ta sa baki 'yan awaren Ukraine su saki masu sanya idanu na kungiyar tabbatar da tsaro da hadin kan Turai ta OSCE da suka kame a gabashin kasar.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bakin kakakinta Stefen Seibert ta ce Berlin ta yi Allah da wannan kamen da aka yi wanda ya saba da dokokin kasa da kasa, inda ta kara da cewar ya kyautu a sako mutanen ba tare da illatasu ba ko gindaya wani sharadi kafin sakinsu.

Merkel din ta kuma shawarci Moscow da ita ma ta yi Allah wadai da wannan kamen da aka yi gami da nesanta kanta daga gare shi, domin a cewarta irin abubuwan da 'yan awaren ke yi a gabashin Ukraine din ya fara wuce makadi da rawa.

A jiya Lahadi dai 'yan awaren suka sako mutum guda daga cikin takwas din da ake tsare da wasu, wadanda hudu daga cikinsu Jamusawa ne.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammad Nasiru Awal