Jamus ta jaddada ƙudirin taimakawa bunƙasar Afirka | Siyasa | DW | 12.04.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Jamus ta jaddada ƙudirin taimakawa bunƙasar Afirka

Jamus na fatan ganin bunƙasar kare haƙƙin ɗan Adam da cigaban dimokraɗiya da kuma siyasa a Afirka

default

Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle da hannun hagu da takwaransa na raya ƙasa Dirk Niebel a ɓarin dama.

Gwamnatin tarayyar Jamus ta jaddada ƙudirin haɗa hannu da Afirka domin taimakawa cigaban nahiyar musamman ta fuskar kyautata haƙƙin ɗan Adam da wanzuwar mulkin dimokraɗiyya da kuma cigaban siyasa.

A ƙoƙarin inganta wannan kyakyawar danganta ce a kwananan Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle tare da takwaransa na raya ƙasa Dirk Niebel suka kai ziyara wasu ƙasashe uku na Afrika wɗanda suka haɗa da Tanzania da Afirka ta kudu da kuma Djibouti inda suka tattauna batutuwan da suka shafi inganta haƙƙin ɗan Adama da dimokraɗiyya da kuma cigaban siyasa a ƙasashen dama nahiyar ta Afrika baki ɗaya.

Günther Nooke

Guenther Nooke, mai baiwa shugabar gwamnatin Jamus shawara kan alámuran Afirka

Mai baiwa shugabar gwamnatin Jamus shawara kan alámuran Afirka Günter Nooke ɗan Jamíyar CDU ya yi tsokaci game da rawar ƙasashe masu cigaban masanaántu na duniya wato G8 suke takawa wajen taimakawa nahiyar Afirka. Batutuwan da ƙungiyar ta G8 ta sha tattauna su a zauruka da dama na ƙasa da ƙasa. Nooke yace wasu daga cikin waɗannan manufofi sun yi tasiri sosai ga cigaban Afrika.

Alal misali yace a taron da aka yi a Glenegales na ƙasar Scotland an ɗauki ƙudirin samar da maƙudan kuɗaɗe domin taimakawa Afirka. Bugu da ƙari a wata haɗuwar da aka yi a Heiligendamm a nan Jamus itama ta ƙasance mai muhimmanci ga Afirka domin kuwa a wannan taro ne aka yanke ƙudirin faɗaɗa wakilcin ƙungiyar G8 ta ƙasashe takwas masu cigaban masaánatu zuwa ƙasashe 20 na duniya. Manufa kuwa ita ce domin shigar da ƙasashen Afirka. A saboda haka muhimmancin Afirka ga nahiyar turai dama dukkanin ƙasashe masu tasowa ta fi gaban a baiyana. Sai dai a gefe guda sakatariyar ƙungiyar kare haƙƙin bil Adama reshen Jamus Monika Lüke na mai raáyi da cewa

" Ana ta maganar tattalin arziki amma bamu ji ana maganar kare haƙƙin bil Adama ba".

A cewar Günter Nooke halin da ake ciki a Afirka batu ne mai sarƙaƙiya, babu shakka akawai buƙatar baiwa nahiyar tallafi, amma ba wai a keɓe wani kasafin kuɗi da zaá riƙa bata a ko da yaushe ba. Abu mafi muhimmanci shine yadda nahiyar zata haɓaka tattalin arzikinta da yaƙi da talauci da samar da muhimman buƙatun rayuwa ga alúma. Waɗannan su ne matsalolin idan ka duba sai ka ga shin me yasa har yanzu Tanzania take cigaba da kasancewa ? cikin talauci ai waɗannan matsalolin ne.

Nooke ya ƙara da cewa a ɗaya ɓangaren ina ganin akwai buƙatar yin sassauci akan tarnaƙin da ake samu na harkokin cinikayya.

A waje guda kuma abin farin ciki shine nahiyar Afirka ta rungumi shirin nan na sabon ƙarni na bunƙasa cigaba wato Millenium development goal wanda ake so a cimma nan da shekara ta 2015. A ƙarƙashin wannan tsari ƙasashen turai ciki har da Jamus zasu bada ɗigo biya cikin ɗari na abin da suke samarwa a shekara a matsayin gudunmawar jin ƙai don tallafawa nahiyar Afirka. A yanzu haka mun kai ɗigo huɗu cikin ɗari wanda abin ƙarfafa gwiwa ne.

Deutschland Amnesty International Generalsekretärin Monika Lüke

Monika Lüke Sakatariyar ƙungiyar Amnesty reshen Jamus

A saboda haka idan muka yi waiwaye adon tafiya game da ziyarar da muka kai wasu ƙasashen Afirka, zaá iya cewa an sami cigaba mai maána a dangantakar dake tsakanin Jamus da ƙasashen na Afrika.

A ɗaya hannun sakatariyar ƙungiyar Amnesty reshen Jamus Monika Lüke ta ce an gabatar da sabbin manufofi kan haƙƙin ɗan Adam sai dai kuma da sauran gyara.

" Muna da masaniyar cewa a manufar gwamnati dangane da Afirka an bada muhimmanci akan batun kare haƙƙin bil Adama, to amma abin nufi shine ba wai kare haƙƙin fursinonin siyasa ba, wajibi ne a samar da magungunguna ga masu fama da cutar AIDS ko SIDA a Afirka ta kudu da Tanzania, kauyuka kuma a samar musu da ruwan sha mai tsabta.

Mawallafa : Ute Schaeffer / Abdullahi Tanko Bala

Edita : Umaru Aliyu