Bikin ranar ma′aikata ta duniya | Labarai | DW | 01.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bikin ranar ma'aikata ta duniya

A wannan Alhamis din ce ake gudanar da bukukuwan ranar ma'aikata ta duniya, don duba irin matsalolin da ma'aikata ke fuskanta da nufin magance su.

Shi dai wanan biki ya samo asalinsa ne kimanin shekaru 140 da suka gabata bayan wata gwagwarmaya da ma'aikata suka yi a birnin Chicago na Amirka a wancan lokacin don ingata yanyin aiyyukan da suke yi.

Wannan biki na bana dai ya zo wa ma'aikata da 'yan adawa da ke kasar Cambodia a karkace domin kuwa bayan fara gangami jami'an tsaro sun far musu har ma suka yi musu dukan kawo wuka da kulaken da suke dauke da su..

Wannan kuwa ba zai rasa nasaba da hanin da mahukuntan kasar suka yi na yin dukannin wani gangami a kasar ba tun cikin watan Janairun da ya gabata, musamman ma dai a dandalin nan na 'yanci da ke fadar gwamnatin kasar.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Umaru Aliyu