AU ta bada umurnin kwance damarar yakin yan kungiyar Janjaweed a Darfur | Labarai | DW | 16.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

AU ta bada umurnin kwance damarar yakin yan kungiyar Janjaweed a Darfur

Kungiyar tarayyar Afrika Au,tayi kira ga gwamnatin sudan data gaggawauta karban makaman mayakan larabawa na janjaweed,dake da goyon bayanta,wadanda kuma ke cigaba da kai hare hare a Darfur.Bayan ganawar hadin gwiwa da hukumar kula da tsagaita wuta ta hadin gwiwa akan Darfur,a birnin Adisa baba,mataimakin shugaban hukumar Monique Mukaruliza ta bayyana cewa ,mahalarta taron sun bada shawarar fara kwance darar yakin mayakan janjaweed din ba tare da bata lokaci ba.Ta fadawa manema labaru cewa,sun samu rahoton commandojin rundunar soji dake Sudan din cewa,gwamnatin Khartum na cigaba da bawa mayakan jamjaweed din makaman fada.Adangane da hakane Mukaruliza tace,idan har an tabbatar da hakan zaa dauki matakan hukunci,daya hadar da kakaba takunkumi wqa wadanda keda laifi.